Tuesday, June 17, 2008

Menene Hukuncin Tabarruki (Neman Albarka)

Tambaya:
Menene Hukuncin Tabarruki (Neman Albarka)
da duk wani abu da yashafi Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, a Lokacin dayake da rai, da bayan mutuwarsa, da tabarrukin da Sahabbai sukayi da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a lokacin rayuwarsa, kuma shin hakan ya tabbata a bayan rasuwarsa? kuma naji cewa Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yaba wani bargonsa, kuma a binne wani dashi a bayan mutuwarsa? kuma shin yatabata cewa Abdullahi dan Umar yayi tabarruki da mimbarin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam? kuma meye ra'ayinku gameda wanda yake cewa yanada gashin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam?.
Malami da ya amsa:
Ustaz Dr. Khalid almushaiqih
Rana: Alhamis 30 Rajab 1427 A.H
Lambar Fatawa: 16619.
Daga: shafin www.almoslim.net
AMSA:
Dukkan yabo da godiya sun tabata ga Allah Mahaliccin Bayi, tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da Alayensa da Sahabansa gabaki daya. bayan haka:
Yin Tabarruki da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam a lokacin da yake da rai, ya kunshi nau'i guda biyu na Albarka, Albarka tashi da kansa da Albarka ta ma'ana.
Amma neman albarka tashi ta kansa: To Sahabai Allah yakara Yarda agaresu, sun kasance suna yin tabarruki da Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, saboda Allah Subhanahu Wata'ala yasanya albarka agaresa, kamar yanda hakan yazo a cikin Hadisin Bukhari da Muslim da waninsu, cewa sunayin tabarruki da Gashinsa da Yawunsa da kakinsa da guminsa da tufafinsa da sauransu.
Nau'i na biyu kuma shine: yin Tabarruki na Ma'ana, Annabai Sallallahu Alaihi Wasalllam, Shine mafi girman dalili ko sababi ga al'ummarsa na samun Albarka ta hanyar karantarda su da shiryar dasu da fitar dasu daga duhu zuwa gas haske. to amma bayan wafatinsa, to Albarka ta ma'ana ta yanke, sedai abinda aka ruwaito daga wasu daga cikin Sahabbai Allah yakara masu yarda, cewa sun kasance sun kiyaye wasu daga cikin abubuwa na Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam kuma sunayin Tabarruki dasu kamar yadda yazo a cikin Sahih Abukhari, daga Ummu Salamah Allah yakara yarda agareta, tanada abun wuya na azurfa ta kiyaye gashin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a ciki, to irin wadannan alamomi ko abubuwa, sahabbai sun kasance, sun kiyiyesu. To amma a Yau: irin abinda shuwagabannin Sufaye suke ik'irari da y'an damfara na cewa sunanan da wani sashi na gashin Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, ko tufafinsa ko makamancin haka, duk k'arerayine da basu da wata kamshin gaskiya, saboda basu da wani dalili -wato hujja akan hakan- ingantatta a cikin Shari'a ta sanadi, to saboda haka babu wani abinda yarage face, Albarka ta ma'ana, ta neman Albarka da abubuwan daya fuskantar, da abubuwan dayayi umarni dasu da abubuwan dayayi hani dasu da tsayuwa akan Sunnarsa da nisantar Sab'a masa. kuma ga Allah muke neman dacewa.

No comments: